Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Amurka Bata Maida Martani Ba


Trump

Har izuwa yanzu dai jami’an gwamnatin Donald Trump basu yi wani martini dangane da karyata zargin da Shugaban kasar yayi wa tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama na Satar Sauraron Waya ba a yayin da ake gudanar da kamfe na zaban bara.

Mai Magana da yawun Obama ya gabatar da bayani a rubuce bayan jerin rubutun twitter da Trump yayi a safiyar jiya asabar na zargin “Obama yayi satar sauraron waya ta a Trump Tower” a Birnin New York kafin zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Nuwambar bara.

Wani mai taimakawa Obama ya ce Zargin da Trump yake yi “karyace kawai”

Kevin Lewis mai Magana da yawun Obama ya ce “ Babu wani jami’in gwamnati a White House lokacin gwamnatin Obama da ya shiga cikin binciken ma’aikatar shari’a, inda ya kara da cewa a bangaren tsohon shugaban kasar ya jaddada hana yin hakan wanda yake dokace da bata wuce kan kowa ba.

Muryar Amurka ta tuntubi jami’an White House domin neman bayani a jiya asabar din amma abin yaci tura. Haka kuma Ma’aikatar tsaro ta F.B.I zuwa Ma’aikatar shari’a basu bada wani bayani dangane da al’amarinba.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG