Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Bauchi ta Zargi Wadda ta Shude da Yin Almubazaranci da Kudi


Malam Isa Yuguda, tsohon gwamnan Bauchi da ake zargi da yin watanda da nera biliyan 91 cikin shekaru takwas

Gwamnatin Bauchi ta yanzu tana zargin wadda da shude a karkashin Malam Isa Yuguda da yin almubazaranci da dukiyar jama'a na bliyoyin nera

Malam Yakubu Ibn Muhammad mai tallafawa gwamnan jihar Bauchi akan harkokin labarai ya yiwa Muryar Amurka karin bayani akan zargin da su keyi na cewa gwamnatin da ta shude ta yi facaka da nera biliyan casa'in da daya d sunan tsaro cikin shekaru takwas.

Daga shekarar 2007 zuwa ta 2015 gwamnatin da ta shude ta kashe wasu kudade da sunan harkokin tsaro ckin shekaru takwas..

Malam Muhammad yace manufarsu ita ce su nunawa jama'a irin kudaden da aka kashe da sunan samarda tsaro.

A cewar Yakubu Ibn Muhammad gwamnan jihar na yanzu ya rantse duk kudin da aka kashe akan hanyar da bata dace ba to sai an dawo dasu. Gwamnatin zata bi duk hanyoyin da suka wajaba domin a samo kudaden.

Alhaji Salisu Tafawa Balewa wani tsohon kwamishana a gwamnatin da ta shude yace duk kudin da tsohuwar gwamnati ta kashe sai da ta sami amincewar majalisa. Yace kamata ya yi jama'ar jihar su gane cewa kare rayukan jama'a da lafiyarsu da dukiyoyinsu abubuwa ne da suka rataya a wuyan gwamna. Idana aka yi la'akari da irin zaman lafiyar da jihar ta samu da kuma abubuwan dake faruwa a jihohi dake mkwaftaka da ita batun kashe kudi akan harkokin tsaro ba wani abu ba ne da za'a cigaba da yin ccekuce akai.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:25 0:00
Shiga Kai Tsaye

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG