Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Borno na Kokarin Gano Yara Mata da Aka Sace


Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima.
Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima.

Yayin da Wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda Biu ya zanta da gwamnan Borno dangane da yara mata da aka sace daga makarantarsu dake Chibok, gwamnan ya bada tabbacin cewa sun dauki matakan gano yaran da nufin kubutarda su.

A wata fira da wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda Biu yayi da gwamnan Borno Kashim Shettima ya nanata anniyarsu da kokarin da su keyi domin kubuto yara matan da aka sace.

Kamar yadda gwamnan yayi bayani kawo yanzu dai an ansamo guda goma sha hudu. Hudu sun diro ne daga motar yayin da ake tafiya dasu. Guda goma kuma sun kubuta wani Lawani ya gansu ya kaisu wurin hukuma.

Gwamnan yace an bude takardar ragista inda iyaye zasu rubuta sunayensu da na 'ya'yansu da basu gani ba. Iyaye hamsin sun riga sun yi ragista ko. Gwamnan yace yayi magana da shugaban makarantar da kuma hakinmin garin Chibok. Shi kanshi gwamnan yana shirin zuwa garin na Chibok domin ya gani menene zasu iya yi.

Dangane da kokarin da gwamnati ke yi na gano yaran gwamnan yace bai cancanta ya bayyana abun da su keyi a bainar jama'a ba. Yace dole a yabi jami'an tsaro domin kokakrin da suke yi. Yace a dinga tayasu da addu'a. Babban abun da ya fi damunsa shi ne samun yaran lafiya ba tare da cin mutuncinsu ba.

Gwamnan yace babu wani addini Musulunci da Kiristanci da ya yadda a sace yara a yi masu fyade. Yace jahilci ne kadai zai ba mutum irin wannan zarafin.

Ga rahoton Haruna Dauda Biyu.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG