Accessibility links

​Litinin dinnan misalin karfe tara na dare zuwa wayewar gari Talata, wasu ‘yan bindiga suka kai hari akan garin Cibok dake kudancin Borno, inda suka kona gidaje da ma’aikatu da wata Makarantar Sakandarin Gwamnati ta mata dake cikin garin.

Wani mazaunin garin ya shaida wa Muryar Amurka cewa maharani sun kona gidajen mutane da dama, suka kuma kona makarantar matan kurmus, sannan suka kwashe matan da kiyasinsu aka ce ya kai dari biyu, suka kuma shiga daji dasu, sannan kuma akwai wasu mata da suka fantsama cikin daji wadanda yanzu haka an shiga nemansu.

Wadannan dalibai na rubuta jarrabawar karshe ne, ta fita daga Sakandare.

A watan jiya ne, gwamnatin jihar Borno ta bada sanarwar rufe duka makarantun Framari har dana Sakandari a wani mataki da ake gani tamkar na kariya ne.

Wannan hari na garin Cibok ya jefa mazauna garin a cikin wani hali na tsorata da fargaba, ganin yadda wadannan mahara suka yi abunda suke so, batare da sun samu wani dauki ba.

Wani wanda baya so a fadi sunnansa yace “jiya misalin karfe tare ne, suka (‘yan bindiga) shiga cikin garin Cibok, sukayi ta mana barna, suka tattara ‘yan matan da suke rubuta WAEC nasu, suka zuba su a cikin motar Roka.”

“A cikin dari biyu, wadanda aka samu basu fi goma sha biyar ba. Jami’an tsaro kuma sun gudu sun buya”, a cewar mutumin.

Kwamishinan ‘yan Sandan jihar Lawal Tanko, ta wayar tarho ya shaida wa Muryar Amurka cewa “mun ji ance an kai hari a Cibok na tura amma har yanzu wadanda na tura basu dawo ba, saboda haka babu abunda zan iya cewa akai.”

Wannan lamari dai na hare-hare, na kara jefa mutanen yankin arewa maso gabashin Najeriya cikin wani hali, musamman ma yadda lamarin ke fadada a cikin kauyuka da ma wasu manyan garuruwan.

Ya zuwa yanzu babu wanda ya dauki alhakin wannan hari.
XS
SM
MD
LG