Gwamnatin jihar Borno ta karbi wasu mayakan 'yan Boko Haram su 14 da suka aje makamansu, wadanda da farko suka kaikansu tare da iyalansu ga hukumomin jamhuriyar Nijar, kafin daga bisani a mika su ga gwamnatin tarayyar Najeriya.
A cikin wadannan mutane 25, akwai maza 14, da mata 3, da kuma kananan yara 8.
Manjo Janar Bamidele,ne jami'in sojan Najeriya da ya karbo wadannan mutane daga jamhuriyar Nijar ya mika su ga gwamnatin jihar Borno. Ya kuma shaida wa Muryar Amurka ce wa wadannan mutane, da kansu suka aje makamai, sannan suka mika kansu domin rungumar zaman lafiya.
Ya kara da cewa an basu horo na musamman a garin Diffa, sannan gwamnatin Nijar ta tuntubi Najeriya da ta karbi wadannan mutane, a matsayinsu na 'yan Najeriya domin a mayar da su gida.
Manjo Janar Bamidele ya yi kira ga 'yan Boko Haram wadanda har yanzu suke cikin daji, da sufito, su mika kansu, za a karbe su hannu biyu, idan sun aje makamansu, domin a samu zaman lafiya a kasar.
A saurari cikakken rahoto cikin sauti daga jihar Bornon Najeriya.
Facebook Forum