Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Borno Zata Tura Mata 30 Kasar Sudan


<span style="line-height: 22px; background-color: rgb(255, 255, 255);">Kelishuvga ko&rsquo;ra, Eron yuqori darajada boyitilgan uran va plutoniy moddalarini ishlab chiqarishni bas qiladi. Bu moddalar ommaviy qirg&rsquo;in qurolini yasashda qo&rsquo;llanishi mumkin.</span>
<span style="line-height: 22px; background-color: rgb(255, 255, 255);">Kelishuvga ko&rsquo;ra, Eron yuqori darajada boyitilgan uran va plutoniy moddalarini ishlab chiqarishni bas qiladi. Bu moddalar ommaviy qirg&rsquo;in qurolini yasashda qo&rsquo;llanishi mumkin.</span>

Sabili da karancin likitoci mata gwamnatin jihar Borno ta fito da shirin tura dalbai mata 30 zuwa koyan aikin likita kowace kama daga wannan shekarar inda zasu kasar Sudan.

Daga wannan shekara gwamnatin jihar Borno zata dinga tura mata talatin kasashen waje koyan aikin likita.

A wannan shekarar gwamnatin na shirin tura dailibai mata talatin kasar Sudan domin koyan aikin likita. Ayarin farko zasu kasance mata zalla ne kawai domin karancin likitoci mata da jihar ke fama da shi. Gwamnatin tace zasu dinga tura mata talatin kasar Sudan duk shekara kuma zasu kashe ko nawa ne kan harkokin ilimi domin ilimi shi ne gishikin kowace al'umma a duniya.

Da yake amsa tambayar da aka yi masa kwamishanan ilimi mai zurfi na jihar Bello Ayuba yace wannan somi ne. Kowace shekara za'a debi dalibai su je koyan aikin likita domin kada asibitocin jihar su rasa likitoci. Yace sun soma da mata ne domin suna da karancin likitoci mata a jihar fiye da yadda ake tsammani duk da cewa mata suka fi bukatar zuwa asibiti musamman batun haifuwa da kula da yara.

Da can gwamnatin ta tura wasu 25 Indiya koyan karatu. Yanzu suna cigaba a Ingila inda suke koyon tukin jirgin ruwa da aikin injiniya. Gwamnan ya tura mutane 20 su koyo aikin injiniyar man fetur.

Ga rahoton Haruna Dauda Biu.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:17 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG