Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Sojojin Najeriya a Boko Haram - inji Sojan Najeriya - Kashi na Biyu


Wani mutum da yace shi sojan Najariya ne daga Kwanduga a jihar Borno, ya fadi irin abubuwan dake wakana a bayan fage, dangane da yaki da kungiyar tayar da kayar baya da aka fi sani da Boko Haram, a hirar da yayi da Aliyu Mustaphan Sokoto na sashen Hausa. Ga kashi na biyu na hirar.

Soja: Bana aikin Najeriyan Army ina fada duniya ta sani, duk wanda yasa dansa a Najeriya Army ya tura dansa ne, a je a kashe shine don gaba daya "business" suke yi da mu, suna turawa ana kashe mu saboda ayi ta basu manyan kudi da sunan sunayi me? ni tunda na zo wata na uku a kwanduga ban ci Naira dubu hamsin ba har yau, ba’a biya ni abinda yakai Naira dubu hamsin ba, sai inyi kwana hudu a daji inna fada da boko haram, sannan sai a zo a dauki Naira dubu daya wai ana bani, kaduba rainin wayo.

Aliyu Mustaphan Sokoto: Amma manyanka suna samun kudi.

Soja: A fadawa duniya ta sani Najeriyan Army bata shirya yin dealing da ,yan boko haram ba, suna yin kasuwanci ne da boko haram suna samun kudi, suna biyan bukatan su manyan sojojin Najeriya, mu kuma kananan yaran ana binmu ana yanka mu kamar fari. Yanzu sojoji mun shiga abun mamaki wadanda wai muje taimaka musu, shine suka janye suka barmu a daji bullet daya basu harba ba wadanda muka je taimako, suka gudu suka barmu a bakin daga ana rataya manyan bingigogi akan Hilux wanda daga mita dubu biyu zai iya kashe ka su ake harbin mu dasu mu kuma muna amfani da wanda sai ka kai kusa da mutum mita dari ko hamsin kafin ka harbe shi ya sameshi. Mu masu jikin karfe ne? Kokuma bamu da iyaye? Ko kuma iyayen mu basu son mune? Ni idan gidanmu ba’a sona, idan na koma in yaso a kore ni a gidan mu tunda inna zama professional duk wanda ya gadama ya tareni.

Aliyu Mustaphan Sokoto: Saboda haka ka bar aikin soja kennan.

Soja: Ni daga yau dai ba ruwa da aikin soja saidai in ta canja saboda zalunci da suke mana na soja, ba zanje in kashe kaina akan ba ko sisi ba, inda ma ana bani FT na da sauki yanzu haka inda na fito an kashe kusan mutun talatin da tara yanzu haka bamu gansuba. Ina suke? za’a iya maida ransu? Wadanda aka fara kashewa a cikin mu ya yau, gawarwakinsu suna nan an ajiye an gagara kai gawansu gida an gagara biyan komai akansa. Kai! a bada ma two minute na mourning na wanda aka kashe da fari ma ba’a yiba, ana maida mu 'ya'yan kaji muna sadakar da ranmu wani yana hada 'yan canjin sa, Allah ya isa wa Najeriyan Army bazan yafe ba duniya da lahira. Hakkin mu da suke ci, da ran yan uwanmu dasuke kashewa saboda suyi kudi, kowa yaci zai kamu akwai ranar hisabi tana zuwa.

Aliyu Mustaphan Sokoto: Saboda haka kana jin duk saboda wadannan abubuwan ne aka kasa shawo kan mutanena da ake kokarin a yake su kennan ko.

Soja: Wallahi, irin wadannan ne wasu aka gagara, inba abun mamaki ba sojan da yake nan shekara biyar gashi nan tsakanin sa da 'yan boko haram kilometer biyu? Ya gagara gamawa dasu sai ya tsaya wai mu da muka shigo yau yau wai mune zamu zo muyi abunda su suka gagara yi a shekara biyar. Wadannan mutanen ba karfin mu suka fi ba,mu soja’s ne ba karfin mu suka fi ba amma lack of waima ka duba an kawo mana APC guda biyar da muka zo nan da kwamanda yace bai isa ba, a kara masa kayan aiki sai aka cire shi, sai aka dauke APC din aka barmu da kwaya biyu, wannan ba raini wayo ba? Wannan ba ana son a gama damu duk ba? Shi yace bazai iya kai 'yan 'yan mutane ya zubar dasu a daji a kashe suba.


Yau kusan kwanaki hudu kennan Sashen Hausa yake neman hukumomin sojojin Najeriya a ciki harda yawan kiran babban sakataren ma'aikatar tsaron Najeriya, Alhaji Aliyu Noma domin mu basu damar mayar da martani ga wadannan kalaman amma bamu samu ji daga wajensu ba.

Sannu ahankali, zamu kawo muku ragowar wannan hira a kwanaki masu zuwa.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG