Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Buhari Ta Karyata Zargin Karuwar Cin Hanci da Rashawa


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Yayin da kwararru ke tabbatar da zargin karuwar cin hanci da rashawa a Najeriya, ita kuwa gwamnatin kasar karyata zargin ta yi.

A wani rubutaccen martani da mai magana da yawun fadar Shugaban Najeriya Garba Shehu ya rattaba wa hannu Kuma aka raba wa manema labarai, ya ce rahoton da Kungiyar yaki da cin hanci da rashawa ta Kasa da Kasa wato Transperancy International ta fitar, cewa an samu koma baya a yaki da cin hanci a Najeriya, bai yi wa mahukunta kasar adalci ba. Amma kwararru na cewa akwai abin dubawa a rahoton.

Rahoton, wanda kungiyar Transperancy International, tare da hadin gwiwar abokiyar aikinta a Najeriya, CISLAC suka fitar ya ce Najeriya ce kasar da ta zo ta 149 daga cikin kasashe 180 da aka yi wa binciken kwakwaf a ma'aunin cin hanci da rashawa a shekara 2020 wanda ya nuna cewa an samu koma baya da maki 3 domin a baya can Najeriya ta zo ta 146 ne. Wani abu da Shugaban Kungiyar CISLAC kuma babban jami'in Transperancy International a Najeriya, Auwal Musa Rafsanjani ya ce an mayar da batun yaki da cin hanci da rashawa kamar makamin kamfe ne kawai domin jami'an gwamnati suna almubazaranci da dukiyar al'umma ba kadan ba, kuma yawancinsu suna bayanin karya idan suka je gaban majalisar kasar a lokacin da suke bayyana yadda suke aiwatar da kudaden al'umma da aka dora masu alhakin gudanarwa.

Shugaban Kungiyar CISLAC, Awwal Ibrahim Musa Rafsanjani
Shugaban Kungiyar CISLAC, Awwal Ibrahim Musa Rafsanjani

Ita kuwa Shugabar Kungiyar yaki da miyagun dabi'u da ke addabar matasa, Halima Baba Ahmed ta ce a kullum talakan Najeriya shi ake cuta, saboda akan laifi kalilan sai a daure shi shekaru da dama. Halima ta ce mai kudi shi ne dan gata a Najeriya, kuma ba haka ya kamata a yi ba, ya kamata doka ta hau kan kowa komin arzikin mutum.

A lokacin da yake nashi nazarin, kwararre a harkar diflomasiyar kasa da kasa kuma mai sa ido a harkokin gudanar da mulki, Farfesa Usman Mohammed na Jami'ar Baze da ke Abuja, ya ce sai an samu an sa tsauraran dokoki masu kaifi, kuma an tabbatar da dokar akan kowa, kafin mutane suji tsoron ta6a kayan Gwamnati ko kudin al'umma, in ba haka ba to ko ina za a yi cin hanci da rashawa tunda babu hukuncin da ake aiwatarwa akan kowa.

Amma a sanarwar da mai magana da yawun fadar shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar, ya ce ba a yi wa Shugaba Muhammadu Buhari adalci ba, domin ba a ta6a samun Gwamnatin da ta yaki cin hanci da rashawa a kasar irin wannan Gwamnatin ta APC ba.

Saurari Madina Dauda da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:42 0:00


XS
SM
MD
LG