Accessibility links

Gwamnatin Filato Ta Dauki Matakan Tsaro Dangane Da Jana'izar Lar


Solomon Lar

A kokarin tabbatar da yin jana'izar tsohon shugaban PDP kuma tsonon gwamnar jihar Filato Solomon Lar cikin lafiya, gwamnatin jihar ta dauki tsauraran matakan tsaro.

Sabili da jana'izar tsohon gwamnan jihar Filato kuma tsohon shugaban PDP da gwamnatin tarayya da jihohin Benue da Filato Da Nasarawa zasu yi, gwamnatin jihar Filato ta dauki tsauraran matakan tsaro.

Solomon Daushep Lar shi ne gwamnan jihar Filato farar hula na farko. Ban da haka shi ne shugaban PDP na kasa na farko kana gashi ya rike sarautar gargajiyar mutane Tarok a matsayinsa na zama Walin Langtang. Ana ganin jana'izarsa zata jawo jama'a da yawa zuwa jihar ta Filato. Ya zama wajibi gwamnatin jihar ta tabbatar da lafiyar jama'a yayin hidimar binne shi.

Ranar Juma'a mai zuwa za'a dauki gawarsa daga Abuja inda zata tsaya a Nasarawa domin girmamawa kafin ta wuce zuwa Jos.

Kwamishanan yada labarai na jihar Filato Yiljap Abraham ya ce suna shirin karbar baki kaman dubu goma sabili da haka suna bukatar karin jamai'an tsaro da karin kayan aikinsu. Ya ce domin yawan jami'an tsaro yayin bikin watakila mutane ba zasu samu walwala kamar yadda suka saba ba, don haka sai su yi hakuri na dan lokaci har a gama bikin. Duk wani matakin tsaro da ya kamata gwamnati ta dauka ta dauka kuma tana cigaba da daukawa domin jihar ta cigaba da zama cikin koshin zaman lafiya har ma bayan jana'zar

Gideon Barde kwamishanan yada labarai a karkashin gwamnatin Solomon Lar ya bayyana irin ayyukan da suka yi a lokacinsa. Shi ya kafa Gidan Telibijan Na Jihar. Su ne suka gina gini da ake kira Gidan Joseph Gomwalk, gini da yafi tsawo a duk fadin jihar. Su suka gina katafariyar kasuwar da aka kone da madatsin ruwan Shen da dai wasu ayyukan.

Zainab Babaji nada karin bayani.
XS
SM
MD
LG