Gwamnatin Jahar Naija Zata Hukunta Masu Sare Itace

Gwamnatin jahar Naija ta dukufa wajen kare muhalli da yaki da hamada da zaizayewar kasa
WASHINGTON, DC —
A wani kokarin yaki da hamada da zaizayewar kasa, gwamnatin jahar Naija ta dauki matakin hukunta duk wanda aka kama ya na sare itace, baicin haka kuma gwamnatin ta dauki wasu matasa kimanin dari biyar ta tura su jahar Filato domin su koyi dabarun alkinta gandun daji. A tattaunawar su da wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka a jahar Naija Mustapha Nasiru Batsari, kwamishinan kula da muhalli na jahar Alhaji Umar Nasko ya yi karin haske akan dalilin su na daukan irin wannan mataki.
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 03, 2023
'Yan Kasashen Waje Masu Saka Ido A Zabe Sun Fara Isowa Najeriya
-
Fabrairu 03, 2023
Kotu Ta Raba Auren Diyar Ganduje