Accessibility links

Taron Shugabannin Addinai Kan Zaman Lafiya a Jihar Plateau

  • Aliyu Mustapha

Taron shugabannin addinai kan zaman lafiya a jihar Plateau, Nigeria.

Shugabannin addinai sun kamalla taron karfafa bukatar samarda zaman lafiya a tsakanin al’ummar jihar Plateau ta Nigeria.

A kwanan baya ne manyan shugabbanin addinai na yankin karamar hukumar mulki ta Yelwan Shendam a jihar Plateau suka gudanarda wani muhimmin zaman tattauna kan hanyoyin da za’a bi a karfafa akidar zaman lafiya a tsakanin dukkan mazaunan jihar, ba tareda la’akari da addini ko kabilanci ba. Wasu daga cikin shugabannin addinan da aka yi tattaunawar da su sun hada da Rev. Michael Kelong, Imam Abdulkarim Salihu, Rev. Dangida Bunu da kuma Mallam Abdullahi Abdullahi Uncle.
XS
SM
MD
LG