Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Kafa Kwamitin Bincike Kan Harbin Dalibai Tara


Gwamnatin jihar bauchi ta kafa kwamiti mai wakilai goma domin ya binciki sanadiyar rikicin da ya faru a kwalejin ilimi dake garin kangere daya janyo rufe kwalejin dakuma raunata dalibai guda 9 sanadiyar harbinsu da ake zargin sojoji da aikatawa.

kwamitin binciken zai gano irin rawar da mutane dai-daiku kokuma kungiyar mutane suka taka wajen haddasa rikicin, da kuma duba duk wani abu da zai taimaka masa don tafiyar da aikin binciken da kuma sanya duk mutumin da zai taimaka ma kwamitin gudanar da aikinsa.

An baiwa kwamitin wa’adin mako guda don gabatar da rahotonsa dangane da lamarin da ya faru tsakanin sojoji da daliban kwaleji..

Da yake jawabi a taron manema labarai da kungiyar daliban ta gudanar, Comrade Shehu Shetima Umar, shine mataimakin kungiyar ta kasa, kuma shine ya jagoranci taron inda ya bayyana cewa lallai sojoji ne suka harbi wadannan dalibai guda Tara, kuma ya bayyana cewa suna shaida daga asibiti da hotuna dake tabbatar da harbin daliban aka yi.

Dan haka mataimakin shugaban daliban ya bayyana cewa suna bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari, da mataimakinsa farfesa Osinbajo, da mai girma gwamnan jihar Bauchi, Muhammad Abdullahi, da shugaban rundunar sojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai, su kafa kwamitin da zai binciki lamarin.

Kakakin hukumar 'yansanda na jihar Bauchi, Sufurtanda Yusuf Muhammed, ya tabbatar da afkuwar lamarin, shi ma a natshi bangaren mataimakin jami'in hulda da jama'a na rundunar soji, ya bayyana cewa an jawo hanaklin sojojin da ke aiki kusa da kwalejin cewa akwai yamutsi a wurin dan haka ana bukatar kasancewar su.

Domin karin bayani saurari rahoton Abdulwahab Muhammad daga Bauchi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:14 0:00

Facebook Forum

An Sami Karuwar Farashin Kayayyaki A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Shiye-Shiryen Shiga Watan Azumi A Kasar Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Ziyarar Sakatare Blinken A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Al'umomi Sun Koka Game Da Tashin Farashin Kayayyaki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG