Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin jihar Bauchi tana shirin yiwa kimanin yara miliyan biyu rigakafi


Ana digawa wata jaririya maganin rigakafi
Ana digawa wata jaririya maganin rigakafi

Gwamnatin jihar Bauchi ta sayi allurar rigakafi miliyan biyu da dubu dari shida domin shirin rigakafin shekara ta 2012 a jihar

Gwamnatin jihar Bauchi ta sayi allurar rigakafi miliyan biyu da dubu dari shida domin shirin rigakafin shekara ta dubu biyu da goma sha biyu a jihar.

Babban sakataren kiwon lafiya matakin farko a jihar Dr. Nisser Umar ne ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya ya yi da shi a Bauchi.

Bisa ga cewarshi, an kiyasta yiwa kanannan yara miliyan biyu allurar rigakafi a lokacin aiwatar da shirin.

Dr. Umar yace a lokutan baya akwatin sanyi ya zama kalubala sabili da haka gwamnati ta kashe kudi wajen sawo akwatunan sanyi yayinda asusun tallafawa kanannan yara ya tallafa, duk da haka yace akwai kalubala a wannan fannin.

Babban sakataren yace gwamnatin jihar ta dauki matakai domin shawo kan matsalolin da aka fuskanta yayin aiwatar da shirin a lokutan baya, sabili da haka ake kyautata zaton ganin nasarar shirin.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG