Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Kafa Dokar Hana Fita A Duk Fadin Jihar


Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El Rufa'i.

Gwamnatin jihar Kaduna ta saka dokar hana fita a duk fadin Jihar, sabanin sanya dokar da tayi tun da farko a kananan hukumomi biyu.

A cewar wata sanarwa daga fadar gwamnatin jihar, an dau matakin ne a dukan kananan hukumomi 23 domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma daga bata gari dake bi suna fasa ma’ajiyar dukiyar al’umma suna kwashewa.

A halin yanzu dokar ta hana fita da shiga, wanda ta fara aiki nan take zata kasance na sa’oi 24 ne a dukkan fadin jihar har na wani locaci da gwamnati taga ya dace a sassauta.

Wannan na zuwa ne yayinda zanga zangar lumana na neman wasu sauye sauye da suka hada da sauke bangaren ‘yan Sanda na SARS ya rikide ya zama tashi hankali da bata gari suka shiga wawure dukiyoyin al’umma a wasu sassan kasar ke dada zama barazana ga harkar tsaro.

Jihar ta Kaduna dama ta dade tana fuskantar tashe tashen hankula dake jefa al’umma cikin zaman dar dar, dauk da cewa mahukunta da shugabannin addinai da na al’umma da jami’an tsaro na ta tattauna yadda za’a magance wannan matsalar.

Facebook Forum

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG