Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya ta Yi Magana Kan Kashe Masu Zanga Zanga Da Yawa Da Aka Yi


Mataimakin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo

Mataimakin Shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo ya mika sakon ta’aziyyarsa ga masu zanga zangar lumana kusan 12 da jami’an tsaron Najeriya suka harbe har lahira a dandalin mashigar Lekki ya kuma yi alkawarin za a bi musu hakkinsu.

Kalaman na Osinbanjo, wanda ya wallafa a dandalin Twitter a daren Laraba 21 ga watan Oktoba, su ne na farko daga bangaren shugabannin kasar game da harbin da aka yi ranar Talata 20 ga watan na Oktoba a jihar Legas.

Shugaban kasa Muhamadu Buhari, wanda ya yi magana sosai ba akan zanga-zangar da ke mamaye kasarsa, bai ambaci harbe-harben da aka yi a Lekki ba a wata sanarwa da ya fidda jiya Laraba amma ya yi kira da a kwantar da hankali kuma ya yi alkawari yin garanbawul a tsarin ‘yan sanda.

Kungiyar kare hakkokin bil’adama ta kasa da kasa ta Amnesty International a wani rahoton da ta fidda ranar Laraba, ta ce mutune 38 suka mutu a ranar Talata kuma akalla mutune 56 suka mutu a cikin makonni biyu a zanga-zangar neman a rushe rundunar ‘yan sanda ta musamman mai yaki da ‘yan fashi, da aka fi sani da SARS, wacce kungiyar ta Amnesty ta zarga da azabtarwa da kuma kisa.

A makon da ya gabata gwamnatin kasar ta soke rundunar amma hakan bai hana zanga-zangar ba, inda wasu suka bijire wa dokar hana fita da aka sanya ranar Laraba, abinda ya haddasa karin harbe-harbe, amma ba a samu rahoton kisa ba.

Facebook Forum

Labarai masu alaka

XS
SM
MD
LG