Accessibility links

A karshen watan Disambar bara jami'an hukumar EFCC suka kama shugaban majalisar dokokin Kano tare da wasu shugabannin majalisar bisa ga zargin rashin bin ka'ida da dokar kasa kan kasafin kudin jihar.

Ita majalisar ta gudanar da wasu sauye-sauye a cikin kasafin kudin da gwamnati ta gabatar mata na wannan shekarar. wanda kila shi ya sa aka kamasu. Daga baya an sakesu bayan sun kwashe kwana biyu suna amsa tambayoyi a hekwatar hukumar dake Abuja.

Makon da ya gabata gwamnati jihar Kano ta gabatar da kara a gaban babbar kotun tarayya bisa zargin cewa jami'an EFCC na musgunawa wasu jami'an gwamnatin jihar. Barrister Malik Kuliyop Umar shi ne kwamishanan shari'a kuma antoni janaral na Kano ya ce babu wani laifi da aka aikata. Sun je kotu amma ta daga kara zuwa 24 ga watan Fabrairu lokacin da zata saurari korafe-korafen gwamnatin a kan EFCC. Ya ce babu wanda ya ce kada a bincika laifi amma akwai ka'idoji da ake bi. Idan sun ga laifi akwai yadda ya kamata su yi. Akwai kuma irin laifukan da zasu iya bincika. Akwai wadanda bai kamata su duba ba kamar harakar kasafin kudi.Harkar kasafin kudi haraka ce ta 'yan majalisa. Su ne suke da hurumin su yi aiki a kan shi.

Bayan an sako 'yan majalisar sai kuma ana bi ana kirawo kwamishanan kudi a kirawo kwamishanan kasafin kudi duk a kan batun kasafin kudin. Tun da ba wai kudade sun bace ba ne ko kuma an sacesu. Duk babu wannan ila gyarar da aka yi.

Yayin da gwamnati ta kai EFCC kara ita kuma kotun umurni ta baiwa jami'an tsaro cewa lalle su kama ma'aikaciyar nan ta Bankin Skye duk inda suka ganta wato Iya Gana Ibrahim Bukar wadda hukumar EFCC ke zargin hallaka kudin haram kusan nera miliyan arba'in. Barrister Mohammed Salisu Abubakar lauyan EFCC ya ce ta rena kotu domin an bata sammaci ta karba amma ta ki zuwa kotun.Lauyanta ya ce tana asibitin Malam Aminu Kano. An rubutawa asibitin amma ya ce idan ba'a bada lambar katinta ba ba za'a sani ko tana asibitin ba.Lauyanta ya ki ya bada lambar katinta har suka bayyana gaban kotun tarayya. Lauyan ya ce ana yi mata tuhumar sata da sauya takardu da na bogi.

XS
SM
MD
LG