Accessibility links

Gwamnatin jihar Kano ta yiwa kananan yara miliyan 7.6 rigakafin shan inna


Ana yiwa wadansu yara rigakafin cutar shan inna

Gwamnatin jihar Kano ta yiwa kimanin kananan yara miliyan bakwai da dubu dari shida allurar rigakafin shan inna

Gwamnatin jihar Kano ta yiwa kimanin kananan yara miliyan bakwai da dubu dari shida allurar rigakafin shan inna a rukunin rigakafin na biyu.

Mataikamakin gwamnan jihar Dr. Abdullahi Ganduje ne ya bayyana haka jim kadan bayan kammala aikin rigakafin.

Dr. Ganduje wanda kuma shine shugaban kwamitin yaki da cutar shan inna a jihar, ya bayyana cewa, an samu nasarar yiwa kananan yara da dama allurar rigakafin ne sakamakon wayar da kan jama’a da gwamnati ta yi.

Mataimakin gwamnan ya ce an maida hankali sosai a yankunan da aka samu bullar shan inna a jihar da kuma kauyuka da suke kan iyakoki da wadansu jihohi . Bisa ga cewar mataimakin gwamnan, an sami Karin bullar cutar ne sakamakon bukukuwa da al’ummar jihar ke halarta da cudanya da ake yi da mutane daga garuruwa da jihohi dabam dabam.

Dr. Ganduje ya yaba irin goyon bayan da hadin kai da kwamitin ya samu daga sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma da na addinai, da kuma kwazo da ma’aikatan jinya a jihar suka nuna.

Jihar Kano dai tana daya daga cikin jihohin arewacin Najeriya da aka fi samun kananan yara dake dauke da kwayar cutar shan inna.

XS
SM
MD
LG