Accessibility links

Gwamnatin jihar Kano zata maido da tsarin duba gari


Wani yaro yana tsince-tsince a bola

Gwamnan jihar Kano yace za a dawo da tsarin duba gari domin shawo kan cutar polio

Gwamnan jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana damuwa dangane da yaduwar kwayar cutar shan inna a Najeriya, ya kuma bayyana cewa, gwamnatin jihar ta dawo da shirin jami’an kula da tsabtar gidaje da ake kira duba gari da suke shiga gida da nufin inganta tsabtar muhalli da gidajen jama’a.

Gwamnan ya bayyana cewa, “Mun sani cutar shan inna cuta ce dake da alaka da yanayin rashin tsabta, dalili ke nan da muka sake dawo da shirye shiryen tsabtace muhalli”.
Ya bayyana cewa, cutar shan inna ta ci gaba da kasancewa babbar kalubala a fannin lafiya na Najeriya, ya kuma ce gwamnatinshi zata maida hankali wajen takalar wannan kalubalar.

Gwamna Kwankwaso ya kaddamar da kamfen yaki da cutar shan inna a birnin Kano da yace tilas mata su sa hannu idan ana so shirin ya cimma nasara. Bisa ga cewar gwamnan mata suna da kyakkyawar rawar da zasu taka kasancewarsu iyayen yara kuma wadanda zasu iya shiga kowanne sako da dabarar samun goyon bayan abokansu mata da kuma magidanta.

Injiniya Musa Kwankwaso ya yi kira ga iyaye mata su bada hadin kai da goyon baya. Ya kuma bayyana niyar gwamnatin ta hada hannu da kungiyoyin mata a jihar domin ganin nasarar shirin

XS
SM
MD
LG