Accessibility links

Gwamnatin jihar Katsina ta shiga yaki da zazzabin cizon sauro


Ana bama dan yaro maganin cutar cizon sauro

Gwamnatin jihar Katsina ta dauki matakan shawo kan matsalar zazzabin cizon sauro dake kashe mata masu juna biyu da kananan yara

Gwamnatin jihar Katsina ta dauki matakan shawo kan matsalar zazzabin cizon sauro, wanda ya kasance daya daga cikin manyan dalilan mutuwar mata masu juna biyu da kananan yara a nahiyar Afrika baki daya.

A yunkurinta na shawo kan lamarin, gwamnatin ta zabi jami’an aikin jinya a dukan kanannan hukumomin jihar 34 wadanda zasu kasance ido da kuma kakakin jihar a wannan yunkurin karkashin jagorancin darektan yaki da cututuka na jihar.

Gwamnatin kuma zata hada hannu da cibiyoyin agaji tare da gudanar da gagarumin gangamin wayar da kan jama’a dangane da illar cutar da kuma rawar da al’umma zata iya takawa a wannan yunkurin.

Gwamnatin ta raba gidajen sauro da aka jika a maganai, yayinda aka yi feshin maganin sauro a inda ruwa ke kwantawa. Gwamnatin har wa yau ta sanar da kashe naira miliyan 181 wajen sayen motocin jinyar tafi da gidanka musamman domin aiki da taimakawa mazauna yankunan karkara, wadanda suka fi mutuwa sabili da rashin halin tafiya asibiti idan bukata ta tashi.

Karamin Ministan lafiya, Dr. Ali Pate wanda ya ziyarci jihar domin ganewa idonshi kalubalar da kuma ci gaba da aka samu a fannin lafiya, ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta lashi takobin shawo kan cututukan dake katse hanzarin kananan yara da kuma mata masu juna biyu. Ya kuma bayyana niyar gwamnatin na cimma muradun karni musamman a fannin kiwon lafiya.

Jihar Katsina na daya daga cikin jihohin da aka sake samun bullar ciwon shan inna kwannan nan.

XS
SM
MD
LG