Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin jihar Katsina tana shirin yiwa yara sama da miliyan biyu rigakafin shan inna


Za a yiwa yara miliyan biyu rigakafin shan inna

Gwamnatin jihar Katsina tana shirin yiwa kimanin kananan yara miliyan biyu da dubu dari shida rigakafin shan inna a jihar.

Gwamnatin jihar Katsina tana shirin yiwa kimanin kananan yara miliyan biyu da dubu dari shida rigakafin shan inna a jihar.

Shugaban kiwon lafiya matakin farko na jihar Dr. Mu’awuya Aliyu ne ya sanar da haka yayin kaddamar da shirin rigakafin a karamar hukumar Batsari. Bisa ga cewarshi, an raba isasshen maganin allurar rigakafin a dukan kananan hukumomi ya kuma yi kira ga iyaye su bada hadin kai.

Dr. Aliyu ya kuma bayyana cewa, an tura sama da ma’aikata dubu dari dukan kanannan hukumomin jihar domin gudanar da aikin rigakafin.

A cikin jawabinshi yayin kaddamar da shirin, shugaban karamar Hukumar Batsari Lawal Agwanko ya jadada niyar gwamnatocin jihar na kananan hukumomi da kuma jiha, wajen ganin nasarar shirin.

Idan za a iya tunawa, san sami wadansu kananan yara biyar dauke da cutar a wadansu kanananan hukumomi na jihar, abinda ake dangantawa da kaurar iyaye daga wadansu jihohi zuwa jihar Katsina da kuma yiwuwar bada hadin kai da wadansu iyaye ke yi.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG