Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar Lagos Ta Kaddamar Da Cibiyar Binciken Kwayoyin Halitta


LAGOS: Gwamnan jihar Legas Akinwumi Ambode
LAGOS: Gwamnan jihar Legas Akinwumi Ambode

Gwamnatin jihar Lagos ta kaddamar da cibiyar binciken kwayar halittar dan adam.Wannan zai taimaka kwarai da gaske wajen warware gardama game da duk wani abu dake da nasaba da jinsi.

Wannan cibiyar itace irinta ta farko a duk fadin nahiyar Afrika Ta Yamma.

Da yake kaddamar da cibiyar, Gwamnan jihar Lagos Akinwumi Ambode yace cibiyar zata taimaka kwarai wajen raba gardama tsakanin ‘yan uwa ko kuma iyaye.

Haka kuma zata taimaka wa ayyukan ‘yan sanda da na shara’a wajen warware shara’oin dake da sarkakiyar mallakar jini ko jinsi.

Karamin Jakadar Amurka dake Lagos, Mr John Brai ya yaba da wannan yunkurin.

Ga Babbangida Jibrin da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00

Facebook Forum

Hira Da Dakta Faruk Bibi Faruk Akan Matsalar Tsadar Rayuwa A Najeriya Kashi Na Biyu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG