Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Legas Zata Sa Kafar Wando Daya Da Bankuna Da Kamfanoni


Gwamnatin jihar legas a tarayyar Najeriya, ta sha alwashin daukar matakan ba sani ba sabo akan manyan kanfanonin kasar dake kasuwanci a jihar, amma kuma suke kin biyan haraji na miliyoyuin Naira, duk da cewa suna cire irin wannan haraji daga ma'aikatan su da kuma kasuwancin su.

Makwanni biyu da suka gabata ne gwamnatin jihar Legas, ta hannun kwamishinan kudi a jihar, Mr Akinyemi Ashade, ta gargadi bankuna da sauran kamfanoni dake gudanar da harkokin kasuwanci a jihar da su hanzarta biyan kudaden su na haraji ada ake binsu wadanda akasari ya zarta na shekaru goma.

Gwamnatin jihar ta sha alwashin daukar matakan ladabtarwa akan su, kodashike kawo yanzu babu wani rahoto dake nuna cewa jami’an gwamnatin jihar sun fara rufe kamfanoni da bankunan, amma wata majiya mai tushe ta kusa da hukumar haraji a jihar ta tabbatar da cewa ba gudu ba ja da baya a wannan mataki da gwamnatin ke niyyar dauka.

Mr Babajide Ishola, masanin harkokin haraji ne, kuma ya bayyana amfanin biyan haraji ga ‘yan kasa da kamfanoni, ya kuma kara da cewa a halin da ake ciki yanzu, kimanin kamfanoni masu biyan haraji Miliyan biyu kacal ake da su, bayan miliyoyin kamfanonin da suka yi rajista da hukumar rajistar kamfanoni, amma basa biyan haraji.

Dan haka bincike ya nuna cewa babu sama da kamfanoni Miliyan goma sha biyar da ke biyan kudadensu na haraji, wanda abin takaici ne, saboda haka wannan mataki da jihar Legas ta dauka a cewar Mr Babajide, zai taimaka wajan samarwa jihar kudaden shiga.

Gwamnatin jihar Legas, na matsawa Kamfanoni domin su biya kudaden harajinne domin suna amsa daga hannun jama’a.

wakilinmu na Legas Babangida Jibrin ya aiko mana da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG