Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Nasarawa bata da niyar kafa dokar hana kiwo


Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Almakura
Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Almakura

Gwamnan jihar Nasarawa Umaru Tanko Almakura yace gwamnatinsa bata da niyyar kafa dokar hana kiwo kamar yadda makwafciyar ta, jihar Benue tayi.

Gwamnatin jihar Nasarawa ta ce bata da niyyar kafa dokar hana kiwo a jihar kammar yadda gwamnan jihar Alhaji Umaru Tank Almakura ya bayyana.

Dokar hana kiwo da gwamnatin Benue ta kafa ta janwo kwararowar makiyaya daga Benuen zuwa jihar ta Nasarawa.

Gwamna Almakura yace tunda aka kafa dokar mutane suna cikin firgita saboda rukunin makiyaya da zasu kauracewa jihar Benue. Domin kada mutane su tagayyara, gwamnan ya kira babban taro da jami’an tsaro da sarakuna da shugabannin kabilu su sanar dasu cewa suna sane da abun da ya faru a Benue kuma jihar a shirye take ta karbi makiyayan da zasu shiga jihar walau su zauna ko su wuce zuwa wata jihar, kamar Filato.

Ya jaddada cewa duk wanda yake son ya zauna suna mara dashi domin jihar bata da niyyar kafa dokar hana kiwo. Yace a fahimtarsu dokar bata da ma’ana. Sai dai zasu sa dokokin da zasu daidaita wuraren noma da kiwo. Dokar zata tanadi hukunci akan wanda ya shiga gona da dabbobi ko kuma manomin da ya shiga burtali ko kuma ya cutar da dabbobi.

Alhaji Muhammad Husseini shugaban kungiyar Fulani reshen jihar Nasarawa yace zasu ba gwamnatin jihar goyon baya wajen kwarmata duk wani makiyayan da ya barrnata gonaki da dabbobinsa.

Peter Ahimba shugaban matasan kabilar Tiv a jihar ta Nasarawa yace fahimtar juna zata taimaka ainun wajen kawo zaman lafiya.

Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG