Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Nasarawa Ta Rusa Gidan Rediyo Mai Zaman Kansa


Bangaren gidan rediyan Breeze 99.9 FM da gwamnatin Nasarawa ta rusa a Lafiya babban birnin jihar

Hukumar raya birane ta jihar Nasarawa ta rusa gidan rediy mai zaman kansa Breeze FM da ya kasance gidan rediyo daya tilo mai zaman kansa a cikin garin Lafiya shi ne ya zama wurin da 'yan adawa da talakawa ke bayyana ra'ayoyinsu tare da gabatar da korafe korafensu kan wasu abubuwa.

A cewar wanda ya mallaki gidan rediyon Mr. Lawali Aboki sun kammala duk wasu matakan gudanar da aikinsu har ma gwamnan jihar ne Alhaji Umaru Tanko Al-Makura ya kaddamar dashi.

Gidan rediyon da gwamna Umaru Tanko Al-Makura ya bude
Gidan rediyon da gwamna Umaru Tanko Al-Makura ya bude

Ranar Juma'a da ta gabata aka mannawa ginin gidan rediyon jan fenti. Washegari ranar Asabar da safe aka rusa gidan rediyon da duka kayan aikin dake ciki.

A cewar Mr. Aboki da misalin karfe takwas ranar Asabar 'yansanda da manyan jami'an gwamnati suka shiga harabar gidan rediyon suka rusashi duk da cewa sun biya harajinsu har na wannan shekarar ta 2017. Suna da takardar mallakar filin da aka gina gidan rediyon da duk wasu takardun da suka kamata suna dasu.

Mr. Aboki yace yana tsammanin gwamnatin jihar ta fusata ne saboda bayyana abubuwan da ma'aikatan kwadago da yanzu suke yajin aiki suke fada. Gwamnati taki a tattauna da ita akan lamuran 'yan kwadagon kuma bata son a tattauna dasu 'yan kwadago.

Gidan rediyon da gwamnatin jiha ta rusa
Gidan rediyon da gwamnatin jiha ta rusa

An yi kiyasin cewa kamfanin rediyon yayi hasarar kumanin Naira miliyan 40 ban da kudin ginin gidan. Wannan na kayan aikin dake cikin ginin ne kawai.

Akan matakin da zasu dauka Mr. Aboki yace zasu hadu a kotu.

Daraktan hulda da mutane na gwamnatin jihar Nasarawa Umar Muhammad Tukur yace gwamnati ta dauki matakin ne kan gine-ginen da ba'a yisu bisa tsari ba.

Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG