Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Neja Ta Mayar Da Almajirai 104 Zuwa Jihar Sokoto


NIGER: Yaran tsangaya da barace barace

"Duk da irin matakan da gwamnatoci ke dauka na hana yawon barace-baracen almajirai, har yanzu wasu mutane na samun hanyoyin yawo da yara almajirai da sunan neman ilimi." 

Gwamnatin jihar Naija da ke Arewacin Najeriya ta ce ta mayar da yara 104 da aka shigo da su jihar daga jihar Sokoto da sunan neman ilmin addini, wadanda za su karkare kan tituna suna barace-barace.

Darakta Janar ta hukumar kare hakkin yara ta jihar, Maryam Kolo ce ta bayyana hakan a Minna, tana mai cewa almajiran da aka mayar suna tsakanin shekaru 4 zuwa 10 da haihuwa, kuma sun yi tattaki ne tun daga jihar Sokoto zuwa Minna a cikin wata mota.

"Hatta da hanyoyin da aka yijigilar almajiran daga nesa, kuma a wannan lokaci na hunturu tambar wani tsagwaron mugunta ne" in ji daraktar.

Ta kara da cewa "duk da irin matakan da gwamnati ta dauka na hana afkuwar ire iren wannan lamari, har yanzu wasu mutane na samun hanyoyin shigo da yara cikin jihar da sunan neman ilimi."

"Muna ba da himma sosai, mun yi matukar mamakin yadda wani zai shigo cikin jihar da yara 104 tun daga Jihar Sokoto zuwa Jihar Neja da sunan neman ilimin Islamiyya ba tare da an ba su abinci ko kudi ba."

Kolo ta kara tabbatar da cewa matakin da gwamnatin jihar ta dauka na hana almajiranci da barace-barace a kan tituna har yanzu yana nan daram.

Yayin da ya ke amsa tambayoyi, malamin da aka sami yaran a hannunsa ya ce ya dauko yaran ne daga garin Illela da ke jihar Sokoto zuwa jihar Neja don yin almajiranci.

Ya ce akwai tsangayar almajirai a Angwan Biri da ke cikin karamar hukumar Bosso na jihar inda yaran za su zauna su yi karatu.

Tun a shekarar 2020 ne gwamnatin jihar Neja ta haramta dukkan nau'o'in barace-barace a fadin jihar, ciki har da almajiranci.

Sai dai kuma rahotanni da dama sun bayyana cewa har yanzu akan samu almajirai a wasu yankunan jihar duk da kasancewar dokar.

XS
SM
MD
LG