Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Neja Za Ta Hukumta Duk Wani Jami'inta da Ya Karkata Takin Zamani


Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello
Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello

Gwamnan jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello ya kaddamar da bikin sayar da takin zamani na bana wanda gwamnatin ta saya kuma ta bukaci a raba ma manoman ainihi akan farashen da ta kayyade tare da yin alkawarin hukumta duk wani jami'inta da ya karkata takin ko ya sayar a wani farashi daban.

Gwamnatin jihar ta sayo takin zamani tan dubu goma sha biyar domin sayarwa manaoma cikin farashi mai sauki na N5,500.

Gwamnan jihar Alhaji Abubakar Sani Bello yace sun sayo takin ne bashi da zummar tabbatar da cewa manoman ainihi sun anfana dashi.

Gwamnan yace a kowace karamar hukuma akwai jami'an da zasu sayar da takin su amso kudi saboda a biya masu taki domin gwamnati ta karbi takin bashi ne. Ya kira mutane su maida hankali da zara sun karbi takin su biya. Ya gargadi mutanen da aka basu amanar raba takin unguwa unguwa da su rike amana. Ya sake nanata manufar gwamnati akan farashen da ta kayyade. Inji gwamnan ba sa son a sayar da takin fiye da N5,500.

Gwamnati za ta sa ido akan yadda aka raba aka kuma sayar da takin kuma duk wanda yayi abun da ba daidai ba ne, wato, ya sabawa umurnin gwamnati za'a dauki mataki bisa ga abun da doka ta tanada. Amma gwamnati za ta ja kunnuwan duk wanda aka damkawa takin ya sayar domin kada yace ba'a sanar dashi ba.

Wasu manoma sun halarci bikin raba takin. Alhaji Shehu Galadiman Kontagora wanda ya kasance shugaban hadaddiyar kungiyar manoman jihar yace sun yi farin ciki domin an shigo da takin akan lokaci da kuma yadda aka tsara rabashi. Yana ganin takin bana zai yi tasiri. Sai dai ya kira gwamnati ta kara lura da yadda za'a sayar da takin saboda sau tari wasu sai su shigo jihar su saya su wuce dashi wani wuri daban. Farashin da gwamnati ta sa, inji Galadiman Kontagora ya dace..

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:15 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG