Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Sokoto Ta Yi Kyautar Gidaje Dubu Daya


Hotun ambaliyar ruwa a Jihar Bauci, wadanda aka dauka Alhamis 15 ga Agusta.

Ambaliyar ruwa a Najeriya musamman a arewacin kasar tamkar ya zama ruwan dare gama gari idan ake asarar rayuka da dukiyoyi sai dai wannan shi ne karo na farko da wata gwamnati zata gina gidaje kayauta.

Ambaliyar ruwa a arewancin Najeriya ba wani abu ba ne sabo. Sau da yawa ana asarar rayuka da dukiyoyi to amma sai dai mahukunta su bada kayan agaji. A wannan karon a jihar Sokoto lamarin ya dauki sabon salo inda gwamnatin jihar ta gina gidaje ma wadanda suka rasa muhallansu.

Mummunar ambaliyar ruwa sanadiyar ballewar madatsar ruwan Goronyo a watan Satumban shekarar 2010 ta shafe kusan garuruwa dari da ashirin a jihar Sokoto ta kuma kakkarya tituna da gadoji bakwai. Lamarin ya kuma haddasa rasa rayuka da dimbin dukiyoyi. Ambaliyar ruwan ya kuma raba dubun dubatan iyalai da matsugunoninsu. Jama'a da dama suka shiga cikin halin ni 'yasu. Bayan bada tallafin kudi da abinci da wurin fakewa gwamnatin jihar Sokoto ta gina gidaje dubu daya a kananan hukumomi uku da bala'in ya fi shafuwa a jihar. Karamar hukumar mulki ta Goronyo ta samu gidaje 400. Gada ta samu 350 yayin da Silami ta samu 250.

Lokacin da gwamnan jihar ke raba gidajen ya ce za'a raba su kyauta ne. Ya ce lokacin da bala'in ya auku mutane sun zama abun tausayi domin basu da abinci kuma basu da wurin kwana dalili ke nan ya sa gwamnati ta kudiri aniyar taimakawa.

Gwamnan jihar Jigawa shi ne ya yi bikin budewa da rarraba gidajen. A jawabinsa gwamna Lamido na Jigawa ya ce abun da gwamnan Sokoto ya yi tamkar ya dawo da muhallin mulki ne a Najeriya domin wasu sun dauka mulki wayo ne ko dabara. Ya ce idan Allah ya cusa ma mutum kishin dan adam to zaka yi anfani da ikonka da kwazonka domin ka gina shi ya yi rayuwar kwarai. Ya ce wannan shi ne shugabanci kuma abun da suke so su dawo dashi ke nan a Najeriya.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00
Shiga Kai Tsaye
LABARI: “Akwai cigaban wannan labari, da wasu labaran masu dumi-dumi, da hotuna, da bidiyo, da cikakkun shirye-shiryen mu duk a shafinmu na www.voahausa.com.”

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG