Cikin wata sanarwa, sakataren gwamnatin jihar Kano, Usman Alhaji ya ce majalisar zartaswar jihar ce ta amince da matakin sauke sarkin da ga mukaminsa.
Usman Alhaji ya kuma ce majalisar zartaswar ta dauki mataki kan sarkin ne saboda ya yi ta saba wa wani sashi na dokokin masarautar Kano.
Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi na biyu ya sha tofa albarkacin bakinsa a kan abubuwa da dama da suka shafi gwamnati da rayuwar al’umma, abinda wasu ke gani ya saba wa ka’idodin aikinsa.
A shekarar 2014 ne sarkin ya karbi ragamar mulki bayan ya rike mukamin shugaban babban bankin Najeriya.
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 26, 2021
Adadin Dalibai Mata 317 Aka Sace A Zamfara - 'Yan Sanda
-
Fabrairu 27, 2021
Jihohin Zamfara, Kano Sun Rufe Makarantun Kwana
-
Fabrairu 26, 2021
Lokacin Lallashin Masu Daukar Makami Ya Wuce- Buhari
-
Fabrairu 26, 2021
UNICEF Ta Yi Allah Wadai Da Sace ‘Yan Mata A Zamfara