Accessibility links

Gwamnatin jihar Kaduna a wani yunkurin inganta tsaro ta haramta sana'ar abacha ko kabukabu a wasu sassan jihar daga ranar 21 ga wannan watan.

Gwamnan jihar Kaduna Alhaji Mukhtar Ramalan Yero ya sanya hannu akan dokar da ta haramta sana'ar achaba a wasu sassan jihar.

Daraktan yada labarai na gwamnan, Alhaji Ahmed Abdullahi Maiyaki yace dokar zata fara aiki daga ranar 21 na wannan watan. Dokar ta shafi wasu sassan jihar ne ba jihar gaba daya ba. Dokar bata hana hawan babur ba amma an hana daukan goyo akan babur. Duk wanda ya karya dokar a karon farko za'a ci shi tarar nera dubu goma ko zama gidan wakafi na wata uku ko kuma duka biyu. Idan aka sake kamashi da karya dokar z'a ci shi tarar nera dubu ashirin ko zama gidan wakafi na wata shida ko kuma duka biyu.

Dangane da wai dokar ka iya kaiga tashin hankali a jihar sai Alhaji Maiyaki yace an yi dokar mai kamannin tasu a wasu jihohi kuma ana nan zaune lafiya kuma ana harkokin yau da kullum. Yace kodayaushe gwamnati tana duba matakai da zata dauka da suka shafi ma fi yawancin al'umma da zasu yi masu anfani, su kyautata tsaro da kuma kawo cigaba a jihar.

Amma shugaban kungiyar kare hakkin Biladama Shehu Sani yace dokar na iya jefa masu sana'ar cikin wani hali. Yace sana'ar achaba ba wai hanyar sifiri ce ba kawai, hanya ce ta cin abinci da wasu suke anfani da ita wurin biya ma kansu kudin haya da kudin makarantar 'ya'yansu da kuma samun abun da zasu ci. Idan an hana aikin mutane da dama zasu wahala. Yace shin yaya za'a hana wannan sana'ar bayan an san gwamnati bata da aiki da zata ba kowa. Bugu da kari, ma fi yawancin masana'antun dake Kaduna an rufesu.

Dan majalisar jihar bangaren masu adawa na jam'iyyar APC Shehu A.B. G. Shawara ya umurci 'yan kungiyar sana'ar abacha da su je wurin gwamna a kungiyance su mika kukansu domin ya duba da idanun rahama yadda za'a taimaka masu da keke napep su samu abun yi. Yace idan an samu an basu keke napep to su yi hakuri domin ba za'a iya ba kowa ba a lokaci daya.

Su masu sana'ar sun ce dokar ta takurasu. Kullum ana son a zauna lafiya amma rashin aikin yi na rura wutar tashin hankali. Suna da iyali da bukatun kansu. Idan an dakatar da su shin gwamnati zata tanada masu wani aikin da zasu yi. Sun ce da sana'a suke biyan bukatunsu da na iyalansu. Idan gwamna ya hana sana'ar to ya samar masu ayyukan da zasu yi.

Tun a makon jiya majalisar dokokin jihar ta tsayar da dokar tana jiran gwamnan ya saka mata hannu domin ta tabbata. Tun da ya saka hannu jiya yanzu dokar ta tabbata ke nan.

Ga rahoton Isa Lawal Ikara.
XS
SM
MD
LG