Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Kasar Afghanistan Tace Ba Zata Amince da Tsagaita Wutar Taliban Ba


Gwamnatin kasar Afghanistan tace ba zata amince da tsagaita wutar da Taliban tace zata yi ba sai ta sanar da ita a hukumance.

Jiya Lahadi, shugaba Asharaf Ghani ya sanar da tsagaita wuta na tsawon watanni uku da Taliban, bisa sharadin cewa kungiyar ita ma tayi haka.

Majiyun Taliban sun bayyana cewa, shugabanninsu sun shaidawa kwamandojinsu su tsagaita wuta na tsawon kwanaki hudu yayin bukukuwan sallah da za a yi wannan makon, sai sai basu sanar da haka a hukumance ba.

Kakakin shugaban kasa Haroon Chakhansoori ya fada yau Litinin cewa, gwamnati zata ci gaba da kai farmaki kan kungiyar Taliban sai shugabannin kungiyar sun sanar da tsagaita wuta a hukumance. Ya kuma ce wa'adin tsagaita wutar da gwamnatin ta diba zai cika a daidai lokacin da kungiyar Taliban ta fara kai farmaki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG