Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Katsina Ta Bullo Da Sabon Tsarin Yaki Da Matsalar Tsaro


Gwamnan Katsina, Bello Masari
Gwamnan Katsina, Bello Masari

A wani yunkuri da take yi na kokarin magance matsalar ‘yan bindiga da suka addabi sassan jihar, gwamnatin Katsina da ke arewacin Najeriya ta ce ta bullo da wani sabon tsarin yaki da wannan matsala ta tsaro da ta ki ci ta ki cinyewa.

Gwamnatin jihar Katsina, ta ce tana shirin fara aiwatar da wani sabon tsari da zai taimaka wajen yaki da matsalar 'yan bindiga da ke kai hare-hare a wasu sassan jihar.

Yayin wata hira da ya yi da Muryar Amurka, shugaban kwamitin tsaro a jihar Dr. Mustapha Inuwa, ya ce za a raya dajin da ya zama mabuya ga ‘yan bindigar.

A cewar Inuwa, daukan wannan mataki zai “ta da dajin daga mafakar wadanda suke amfani da hanyar suna shiga garuruwan Babban Duhu, Lamma, Kurfi da sauran su.

An yake “shawarar cewa, dajin nan a maida shi gonaki, kuma wadanda suke sha’awa a yanka masu su yi gidaje a wurin daga karshe kuma gwamnatin ta fara yin makaranta da asibiti.” In ji Dr Inuwa.

A cewarsa, tuni gwamnati ta ba da umurnin a fara aiki a dajin domin a kawar da manyan itatuwa.

Wakilin VOA Sani Shu’aibu Malumfashi ya ruwaito cewa bisa ga sabon tsarin, za a maida dazukan da maharan ke boyewa ya zama filaye da gonakin noma ne ga maharan da suka tuba ga kuma jamar da suka nuna sha’awarsu.

Shugaban kwamitin tsaron ya kara da cewa, har yanzu kofar yafiya ga maharan a bude take illa dai tsarin ya koma hannun sojojin Najeriya.

Wasu daga cikin jama’ar yankin da lamarin zai shafa, sun yi fatan dorewar wannan tsari da ake kokarin shimfidawa wanda suka ce ya yi daidai idan har zai kawo sulhu da maharan.

Jihar Katsina da ke yammacin arewacin Najeriya ta jima tana fama da matsalar 'yan bindiga a 'yan shekarun nan lamarin da ya yi sanadin mutuwar daruruwa mutane tare da asarar dumbing dukiyoyi.

Sannan daruruwan dubban mutane sun tsere daga gidajensu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG