Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Legas Ta Samu Izinin Daukaka Kara Akan Sako Manjo Al-Mustapha


Manjo Hamza al-Mustapha
Manjo Hamza al-Mustapha

Ranar 12 ga watan bakwai ne a shekarar 2013 kotun daukaka kara ta yanke hukuncin sako Manjo Hamza Al-Mustapha bayan ya kwashe kusan shekaru goma sha biyar yana kulle bisa tuhumar da aka yi masa kan kashe Hajiya Kudirat Abiola

Hajiya Kudirat Abiola ita ce uwargidan Chief M.K.O.Abiola hamshakin attajiri wanda kuma aka kyautata zaton shi ya lashe zaben shugaban kasa na shekarar 1992 a karkashin jam'iyyar SDP.

A wani takaitacen zama da kotun kolin Najeriya tayi jiya Alhamis ta ba gwamnatin Legas izinin daukaka kara akan sako Manjo Hamza Al-Mustapha da aka yi shekaru uku da rabi da suka wuce.

Oluwayemisi Osunsanya wadda ta wakilci gwamnatin Legas a zaman kotun kolin tace sun yi murna an basu izinin daukaka kara. Tace zasu yi aikin kawo shaidu bisa lokaci.

Shi ma Joseph Daudu lauyan Manjo Hamza Al-Mustapha yace sun ki a ba gwamnatin Legas damar da ta nema amma kotun kolin ta basu. Yanzu gwamnatin Legas nada damar daukaka kara cikin kwanaki talatin daga jiya Alhamis.

Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:56 0:00

Zaben 2023

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG