Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Mulkin Sojan Mali Ta Dakatar Da Harkokin Jam'iyyun Siyasa Har Sai Wani Lokaci


Gwamnatin Mulkin Sojan
Gwamnatin Mulkin Sojan

Gwamnatin mulkin sojan Mali ta kafa wata doka da ta dakatar da ayyukan jam'iyyun siyasa, kamar yadda kakakin gwamnatin kasar Abdoulaye Maiga ya bayyana a cikin wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na kasar da yammacin jiya Laraba.

Sanarwar ta ce, dokar ta dakatar da duk wasu ayyukan jam’iyyun siyasa da kuma “kungiyoyi masu nasaba da siyasa” bisa dalilan tabbatar da zaman lafiyar jama’a.

Tun a watan Agustan 2020 ne kasar Mali ke karkashin mulkin soji, wanda shi ne na farko cikin juyin mulki takwas da aka yi a yammacin Afirka da yankin tsakiyar Afirka cikin tsawon shekaru hudu, ciki har da makwabtanta Burkina Faso da Nijar.

Sojojin Mali na yanzu sun kwace ragamar shugabanci ne a wani juyin mulki na biyu a shekara ta 2021 inda daga bisani suka yi alkawarin maido da mulkin farar hula nan da ranar 26 ga Maris, 2024 bayan an yi zabe a watan Fabrairu.

Sai dai a watan Satumban shekarar da ta gabata gwamnatin mulkin sojan kasar ta ce za ta dage zaben na watan Fabarairu har illa masha Allahu, saboda wasu dalilai tsare tsare, lamarin da ya janyo cece-ku-ce tsakanin kungiyoyin siyasa.

Da yawa sun sake mayar da martani bayan wa'adin mika mulki na watan da ya gabata ba tare da an gudanar da zabe ba, yayin da wasu manyan jam'iyyun siyasa da kungiyoyin fararen hula a Mali a ranar 31 ga Maris suka yi kira da a tsai da ranar zaben.

“Za mu yi amfani da duk wata hanya ta doka da ta dace wajen dawo da tsarin mulkin kasarmu kamar yadda aka saba,” a cewarsu a wata sanarwar hadin gwiwa mai dauke da sanya hannu sama da 20 da suka hada da babbar gamayyar jam’iyyun adawa da jam’iyyar tsohon shugaban kasar da aka hambarar.

Tun a baya ne dai mahukuntan mulkin sojan Mali suka saba alkawarin farko na gudanar da zabe a watan Fabrairun 2022.

Saurari karin bayani daga Souley Moumouni Barma:

Gwamnatin Rikon Kwaryar Mali Ta Dakatar Da Duk Ayyukan Jami’un Siyasa.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG