Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Myanmar ta ce kabilar Rohingya Musulmi na iya komawa kasar


'Yan kabilar Rohingya da suka yi gudun hijira daga Myanmar
'Yan kabilar Rohingya da suka yi gudun hijira daga Myanmar

Shekara guda bayan da 'yan kabilar Rohingya musulmi kusan dubu dari bakwai suka arce daga Myanmar domin yadda sojojin kasar ke kashesu, yanzu hukumomin Myanmar din sun ce suna iya komawa kasar daga Bangladesh inda suke gudun hijira saboda kwanciyar hankali da aka samu

Shekara guda bayan da dubun-dubatar Musulmi ‘yan kabilar Rohingya, wadanda tsiraru ne a kasar Myanmar, suka yi tururuwar tserewa zuwa Bangaladesh, domin gujewa farmakin da sojojin kasar suka kai musu, hukumomin Myanmar, sun ce hankula sun yi kwanciyar da ‘yan gudun hijrara za su iya komawa gidajensu.

To amma, masu sa ido na kasa-da kasa, sun ce ba a samu kwanciyar hankalin da ‘yan kabilar ta Rohingyan za su koma muhallan nasu ba.

Wadanda suka tsira daga mummunar azabar da aka ganawa ‘yan kabilar ta Rohingya a watan Agustan bara, sun fadawa masu ayyukan agaji a Bangladesh irin ukubar da suka fuskanta, wadanda suka hada da yadda ake yi wa makusantansu fyade da kisa tare da kona kauyukansu duk a gabansu, ta yadda ba za su yi sha’awar komawa kauyukan nasu ba.

Akalla Musulmi ‘yan kabilar ta Rohingya rabin miliyan ne suka tsere zuwa Bangladesh a watan farko da aka fara kai musu farmakin.

Daga baya, wasu dubu 200 suka bi bayansu cikin ‘yan watannin da suka biyo baya.

Yanzu haka suna nan a wani sansanin ‘yan gudun hijira da ake kira Cox’s Bazar, sansanin da aka yi kiyasin cewa shi ne mafi girma a yawan jama’a, a duk fadin duniya.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta ayyana wadannan hare-hare a matsayin kisan kare dangi, ko da yake, hukumomin na Myanmar sun musanta wannan matsaya da Majalisar ta Dinkin Duniya ta dauka, ta ayyana lamarin a matsayin kisan kare dangi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG