Bayan sun kammala taro da jami'an gwamnatin tarayya, kungiyar masu dakon man fetur ta fitar da wata sanarwa inda tace babu wani tunenen kara farashin mai daga bangaren gwamnati.
A cewar sakataren kungiyar Malam Danladi Fasali gwamnatin Najeriya bata tunenen kara farashi kuma dogon layi da aka fara gani a gidajen mai tsoro ne kawai. Mutane su kwantar da hankulasu.
Danladi Fasali yace abun da ya damesu shi ne bashin da suke bin gwamnatin tarayya na kudi biliyan dari da tamanin kuma gwamnati tayi alkawarin biyansu. Suna kyautata zaton mako mai zuwa ne za'a biyasu'
Ga karin bayani