Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Na Ci Gaba Da Neman Hanyar Sasantawa Da Kungiyar Niger Delta Avengers


Tsagerun 'Yan Niger Delta
Tsagerun 'Yan Niger Delta

Gwamnatin Najeriya tace duk da irin hare haren da ‘yan kungiyar Avengers ta Niger Delta ke kaiwa a tashoshin man Fetur a yankin, tace zata ci gaba da nemo hanyar sasantawa domin kawo karshen wannna matsala.

Sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya Injiniya Babacir David Lawal, yace kofar gwamnati a bude take domin magance wannan matsala, ya fadi haka ne a wani taron manema labarai a Yola, inda ma ya nuna cewa damuwar gwamnati kan lamarin shine rashin sanin su waye shugabannin kungiyar, amma duk da haka gwamnati ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen nemo hanyar sasantawa.

Hare haren na ‘yan Niger Delta dai na ci gaba da durkusar da harkar samar da Mai da kuma wutar lantarki a kasar, sakamakon barnar da suke yiwa tashohin samar da mai.

Hari na baya bayan nan dai shine wanda kungiyar tace ta kai akan tashar kamafanin Chevron na kasar Amurka da kuma kamfanin NNPC mallakar gwamnatin Najeriya. Sai dai kuma ga masu fashin baki na ganin dole ne a hada hannu wajen magance wannan matsala.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

XS
SM
MD
LG