Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Niger Delta Avengers Ta Sake Kai Hari A Wasu Tasoshin Mai


우크라이나 체르니히우에서 군인들이 훈련을 하고 있다. 러시아군이 크림반도 인근 케르치해협을 통과하는 우크라이나 해군 함정 2척과 예인선 1척을 나포하는 사건이 있은 후 러시아와 우크라이나 간의 긴장이 고조되고 있다.
우크라이나 체르니히우에서 군인들이 훈련을 하고 있다. 러시아군이 크림반도 인근 케르치해협을 통과하는 우크라이나 해군 함정 2척과 예인선 1척을 나포하는 사건이 있은 후 러시아와 우크라이나 간의 긴장이 고조되고 있다.

A daidai lokacin da gwamnatin tarayyar Najeriya da sabuwar kungiyar Niger Delta Avengers ko NDA, ke musayar yawu akan shirin, sai kwatsam kungiyar ta fitar da wata sanarwa dake cewa ta kai wasu sabbin hare-hare kan wasu manyan tasoshin mai da iskar gas a yankin na Niger Delta

Kungiyar ta 'yan bindigan ko NDA ta sanar da kai jerin hare-hare a shafinta na yanar gizo.

Kungiyar tace ta kai hari akan tashar man kamfanin Chevron na kasar Amurka da kuma kamfanin NNPC mallakar gwamnatin Najeriya. Kamfanonin su kan tura dayan mai zuwa tashar Warri dake jihar Delta. Tsakanin Asabar da jiya Lahadi kungiyar tace ta kai hare-hare har sau hudu, kuma tayi nasarar lalata bututan mai.

Janar Rabe Abubakar mai magana da yawun rundunar sojan Najeriya ya yi magana akan hare-haren. Yace a matsayinsu na jami'an tsaro dole ne su dauki matakan tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Akan zargin da ake yiwa sojoji wai suna jan kafa, Janar Abubakar yace suna aiki da bin dokoki ne. Ba zasu wuce abun da shugabaninsu suka gindiya masu ba. Amma sojoji suna daukan matakan da suka dace domin kawo karshen tashin tashinar.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG