Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Na Tunanin Sake Sayan Kamfanonin Wuta Da Ta Sayar


Babatunde Fashola, ministan ayyuka, gidaje da makamashi

Gwamnatin Najeriya na tunanin sake sayen kamfanin wutar lantarki musamman DISCO domin inganta samar da wuta a duk fadin kasar

A zaman da majalisar ministocin Najeriya ta yi jiya Laraba a Abuja a karkashin shugaba Muhammad Buhari, gwamnati ta duba wasu batutuwa da suke da mahimmanci.

Bayan taron gwamnati ta bada tabbacin daukan wasu matakan da zasu inganta samar da wutar lantarki a kasar. Matakin ya hada da sake sanya jari cikin kamfanonin dake samar da wutar lantarki.

Injiniya Suleiman Adamu ministan dake kula da ma’aikatar albarkatun ruwa ya ce sun gaji rikici akan harakar wutar lantarki saboda kamfanonin da aka sayarwa harkokin wutar lantarki sun gaza saka jarin da ya dace domin su sayarwa ‘yan kasa wuta wadataciya.

Na farko, kamar yadda ministan ya fada yadda aka sayar da kamfanonin ne bai yi daidai ba saboda an yi son kai da yawa. An sayarwa mutanen da wutar lantarki ba harkarsu ba ce. Abokanai da sauran ‘yan siyasa aka sayarwa kamfanonin.

Ministan ya fada cewa kwanakin baya dole gwamnati ta tanadi Nera biliyan dari bakwai saboda kamfanin DISCO Adake sayan wuta baya biya domin baya karban kudi daga wadanda yake ba wutar. Idan hakan ya ci gaba kamfanin dake sayar masa da wuta da shi DISCO duk zasu durkushe. Kamfanonin dake bada iskar gas sun kansu sun kusa durkushewa. Domin a ci gaba da samun wuta dole gwamnati ta samu kudi ta raba masu.

A cikin tunanen gwamnati matsalar tana tare da kamfanin DISCO ne. Walau gwamnati ta narkar da jarin masu kamfanin ta kara jari akan kashi 40 da take dashi yanzu domin ta mallaki kamfanin ko kuma masu kamfanin yanzu su fadadashi ta yadda wasu kwararru zasu shigo.

Ga hirar da Umar Faruk Musa yayi da Ministan Albarkatun Ruwa

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG