Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Dakatar Da Karin Kudin Wutar Lantarki


Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Gamayyar kungiyoyin kwadagon Najeriya ta dakatar da yajin aikin gamagari da ta fara da misalin karfe 12 na safiyar yau Litinin, wanda da aka tsara zai kai  tsawon makonni biyu. 

Wannan na zuwa ne bayan amincewa da maida kudin wutar lantarki yadda ya ke a da da gwamnatin tarayyar kasar ta yi sakamakon tattaunawar da ta da yi da kungiyoyin a daren ranar Lahadi zuwa karfe 2:50 na safiyar Litinin 28 ga watan Satumba tare da kafa kwamitin da zai yi nazari kan batun karin da kuma sauran bukatun da kungiyar ta kwadago ta gabatar.

Jigo kuma mataimakin sakataren kungiyar kwadago ta NLC, Kwamared Kabir Nasiru, ya tabbatar da cewa sun shiga yajin aiki da karfe 12 na safiya amma sun dakatar da shi zuwa wani dan lokaci.

A bangaren gwamnatin kasar kuma, Ministan kwadago da ayyuka Chris Ngige, da karamin Ministan albarkatun man fetur Timipre Silva, da karamin Ministan kwadago da ayyuka Festus keyamo, da Ministan yada labarai da al’adu Alhaji Lai Muhammad, da kuma sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ne suka rattaba hannu a yarjejeniyar da aka cimma, wadda shugaban kungiyar kwadagon NLC, Ayuba Wabba da takwaran aikinsa na kungiyar TUC, Quadri Olaleye da sauran su suka sa hannu a kan yarjejeniyar.

Shugaban kwamitin amintattu na gamayyar kungiyoyin arewa, Nastura Ashir Shariff, ya ce sun ga sanarwar da kungiyar kwadagon ta fidda ta janye yajin aiki da kuma matsayar da suka cimma da gwamnatin Najeriya kan tabbatar da cewa kudin man fetur ya ci gaba da zama yadda yake a da.

Shariff ya kara da cewa wannan wani abu ne na dan lokaci don haka ya kamata gwamnati ta gyara matatun man fetur idan ba haka ba 'yan Najeriya ba zasu daina shan wahala ba. Abu na biyu shine tallafin da gwamnati ta ce zata saka kan motoci da gidaje, wannan wani abu ne na dan lokaci kuma ba zai dore ba. Na uku kuma shine batun dakatar da karin kudin wutar lantaki zuwa sati biyu abu ne mai kyau da ya kamata a tsaya a yi tsari akan sa.

A cikin makonni biyu za a yi nazari kan kamfanonin da suke samar da wutar lantarki, a yanzu dai za su dakatar da aiwatar da sabon karin kudin wutar lantarkin da aka yi a 'yan makwannin baya da suka wuce.

Gwamnatin tarayya ta ce zata bada tallafi a bangaren sufuri, wutar lantarki, aikin noma, da ayyukan jinkai da zasu taimaka wajen rage radadin da ma’aikata da sauran al’ummar kasar ke ji sakamakon kari a kudin wutar lantarki da cire tallafin man fetur da aka yi.

Saurari cikakken rahoton Halima Abdulra’uf:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00


Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG