Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Fara Kafa Tasoshin Manyan Motoci - Amaechi


Rotimi Amaechi, ministan sufurin Najeriya

A wani shiri na kawar da cunkoson da manyan motoci ke yi akan hanyoyin Najeriya, ministan sufuri yace gwamnati ta fara kafa wa manyan motoci tasoshi.

Inji ministan sufurin Najeriya Rotimi Amaechi gwamnati ta fara aikin kafa madakatan manyan motoci a sassa daban daban na kasar domin kawar da yadda motocin kan cunkushe hanyoyi kamar a wani gari dake kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Kafa tasoshin zai mayar da lamarin tuka motocin irin na zamani.

Hassan Bello wanda ya kasance shugaban hukumar hadahadar kasuwanci ta teku yace wajajen da za'a kafa tasoshin za'a tanada wajen saukan baki, dakunan cin abinci, dakunan shan magani da na jami'an tsaro. Sassan zasu kai kadada hamsin, inji Bello za'a gina su nesa da manyan tituna.

A cewarsa ana shirin da duk kungiyoyin direbobin dake Najeriya domin dole a yi dasu. Yace bayan an gina tasoshin to ba zasu kara zuwa su ajiye motocinsu ko akan hanya ko bayan gari ba. Komi suke bukata a tasoshin zasu samu hatta ma idan suna bukatar makanimai.

Ga rahoton Nasiru Adamu Elhikaya da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:37 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG