Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Kaddamar Da Tagwayen Hanyoyi


Aikin gina gada

Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da tagwayen hanyoyi tsakanin Ibadan da Oyo a kokarin rage haduran motoci a kan hanyoyi kasar.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kaddamar da tagwayen hanyoyi daga Ibadan zuwa Oyo waddanda ministan ayyuka Mr. Mike Onanume ya yi.

Ministan a jawabinsa ya ce waddannnan hanyoyi zasu zama abun alfanu ga jama'ar kudu maso yammacin Najeriya.Ya kara da cewa shimfida hanyoyi masu kyau zai rage haduran motoci da kare rayukan mutane. Ta dalilin hakan gwamnati na kokarin kammala hanyoyin daga birnin Ibadan a jihar Oyo zuwa Ilori a jihar Kwara.Mr. Mike Onanume ya ce gwamnatin tarayya na kokarin gyara duk manya manyan hanyoyin kasar yadda motoci zasu rika tafiya a kansu lami lafiya ba tare da wata matsala ba.Shi ma gwamnan Oyo wanda sakataran gwamnatin Mr. Akin Olajide ya wakilta cewa ya yi gwamnatin jihar zata hada hannun da gwamnatin tarayya domin samar ma jam'ar jihar abubuwan more rayuwa.

Direbobin jihar Oyo sun bayyana jin dadinsu da kaddamar da tagwayen hanyoyin. Sun ce hanyoyin zasu rage hadura a Ojo wurin da aka fi samun munanan haddura da kuma bukatar a cigaba da gina irin wadannan hanyoyin a kasar.

Tagwayen hanyoyin masu tsawon kilomita 43 da aka bada kwangilarsu tun shekarar 2001 sun riga sun lakume nera biliyan ashirin kana suna cikin hanyoyin da suka hada jihar Oyo da jihar Kwara.

Hassan Umar Tambuwal nada karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:18 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG