Accessibility links

Yajin Aikin Ma'aikatan Man Fetur a Najeriya ya sa Jama'a cikin Kunci


Masu zanga-zanga a Kano

Yajin aikin ma'aikatan man fetur a Najeriya ya sa jama'a cikin kuncin rayuwa sabili da rshin samun man da kuma tsadarsa a kasuwar bayan fagge inda 'yan cuwa-cuwa ke cin karensu ba babbaka

Da zara ma'aikatan man fetur sun shiga yajin aiki a Najeriya sai matasa su bazama suna cuwa-cuwar sayar da mai a farashen da kan ninka kusan sau biyar ma jama'a da ikirarin wai taimako ma suke yi. Lokacin yajin aikin gidajen mai, sukan kasance basu da man amma abun mamaki sai a ga matasa suna sayarwa a kasuwar bayan fagge da aka fi sani da "black market" a turance.

Yajin aikin kwana uku da ma'aikatan man fetur suka shiga ya farfado da wannan kasuwar bayan faggen. Lokacin yajin aiki wasu ma'aikatan gidajen mai kan faki idanun masu yajin aikin su sayar da man da suke da shi cikin dare wanda yin hakan baya rasa nasaba da kungiyar ma'aikatan man nupeng da kuma kungiyar masu sayar da man ipman.

Wani Abdullahi Garba Baba Dangaye ya shigo Abuja daga arewa maso gabas da murmushi amma murnarsa ta koma ciki sabili da kuncin rayuwa da ya shiga domin karancin man fetur. Yayin da yake maida martani cewa ya yi yakamata a ce shugaban kasa nada masu bashi shawara game da ma'aikatan aikin man fetur su bashi shawara yadda za'a zauna da ma'aikatan a fahimci juna kafin su kai ga yajin aiki. Ya ce idan ana wuyar mai a Abuja to dole ne ma a yi wuyarsa akoina akasar. Ya kara da cewa idan a nera 97 man na wuyan samu sai ya kai nera 1000 za'a samu?

Jama'a na fatan yajin aikin zai tsaya a kwana uku kamar yadda ma'aikatan suka fada domin farashin kaya ya soma tashi gabannin karatowar azumi da za'a fara makon gobe. Motocin da zasu kawo kaya cikin garuruwa kamar Abuja basu samu sun shigo ba don haka 'yan kasuwa sun soma sayar da kayansu da tsada.

Bisa ga duk alamu babu samun nasarar dalilin shiga yajin aikin wajen tilasta wa kamfanonin man ketare su dena sa ma'aikatansu bauta da hanasu cin gajiyar kungiyanci da kuma gyara manyan hanyoyi domin a rage hadduran mayan motoci a Najeriya.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

XS
SM
MD
LG