Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Kaddamar Da Wani Shirin Samar Da Ayyuka Ga Matasa


Sunday Akin Dare, Ministan Matasa da Wasanni
Sunday Akin Dare, Ministan Matasa da Wasanni

Ya zama wajibi gwamnatin tarayya ta yi amfani da karfin yawa da kwazo- matasa wajen rage hasturan matsalar tsaro a kasa.

Ministan lamurran ci gaban matasa da wasanni na Najeriya Sunday Akin Dare ya kaddamar da wani sabon shirin samar da ayyukan yi ga matasa na shekarar 2021 zuwa 2024 a Abuja.

Ministan ya ce kaddamar da shirin yana nuni da jajircewar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen samar da ayukan yi har miliyan 3.7 a duk shekara, da kuma cimma muradun ci gaban kasa, musamman ta fannin tattalin arziki mai dorewa.

"Ya zama wajibi gwamnatin tarayya ta yi amfani da karfin yawa da kwazo- matasa wajen rage hasturan matsalar tsaro a kasa," in ji minista Dare.

Ya kuma kara da cewa kamata a yi amfani da matasa a matsayin jarin da kan iya samar da ci gaban tattalin arzikin al’umma, a maimakon ba su wasu kananan ayyuka lokaci zuwa lokaci.

Ministan ya bayyana takaicinsa dangane da matsalar rashin ayukan yi da matasa a kasar ke fama da shi, inda ya ce tasirin matsalar bai tsaya a bangaren matasan kadai ba har da matsalar talauci da koma baya da kasar ke fuskanta.

XS
SM
MD
LG