Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Musanta Zargin Neman Cin Hancin Dala Miliyan 150 Daga Kamfanin Binance


Shugaban Najeriya, Bola Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu

Sanarwar da ta musanta zargin, wanda mai magana da yawun Ministan Yada Labarai, Rabi'u Ibrahim ya sa hannu, ta ce bita da kulli ne kawai, kuma kage kamfanin ya yi wa gwamnatin ko kuma jami'anta.

ABUJA, NIGERIA - Gwamnatin Najeriya ta musanta zargin da shugaban kampanin Hadahadar Kudi ta Yanar gizo Binance, Richard Teng ya yi cewa, wasu jami'an gwamnatin Tinubu sun nemi cin hancin dalar Amurka miliyan 150, domin a yi wa kamfanin sassauci a shari'ar da ake yi da shi a kasar.

Sai dai Masu ruwa da tsaki a fanin yaki da cin hanci da rashawa sun ce wannan zargi bai zo musu da mamaki ba.

Sanarwar da ta musanta zargin wanda mai magana da yawun Ministan Yada Labarai, Rabi'u Ibrahim ya sa hannu, ta ce bita da kulli ne kawai, kuma kage kamfanin ya yi wa Gwamnatin ko kuma jami'anta.

Rabi'u ya ce babu gaskiya ko kadan a zargin inda ya kara da cewa wata kutungwila ce da kamfani ya yi domin hana a bincike shi, tunda ana zargin kamfanin na ba da kafa ne ta yi wa kasar barna da zagon kasa wajen lalata arzikin ta.

An kwashi tsawon lokaci ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkar tsaro Nuhu Ribadu yana takun saka da jami'an kamfanin Binance kan kin biyan haraji da kuma karkatar da kudade da ba 'a fadi adadin su ba, wani abu da ya sa har wani jami'in Binance Nadeem Anjarwalla ya gudu daga Najeriya amma aka kamo shi daga kasar Kenya makonni hudu da suka gabata, kuma tun lokacin ne ake tafka shari'a da kamfanin.

Akan haka ne shugaban kamfanin Richard Teng ya yi zargin an nemi cin hanci har na dalar Amurka Miliyan 150 daga wurin su, domin a wofantar da binciken.

Auwal Musa Rafsanjani wakilin Kungiyar Transparency International mai yaki da cin hanci a kasa da kasa, ya bayyana wa Muryar Amurka ra'ayinsa game da al'amarin cewa wannan bai zo masa da mamaki ba, ganin yadda cin hanci da rashawa ya yi kaka-gida a kasar.

Rafsanjani ya ce akwai alamu, domin yanzu haka ana tuhumar wasu manyan jami'an gwamnati da tafka cin hanci da rashawa har da kuma cin amanar kasa.

Rafsanjani ya ce gwamnati ba ta da wata tsayayyar akida ta yaki da cin hanchi da rashawa, inda ya yi kira ga Richard Teng da ya fito ya bayyana sunayen wadanda suka nemi cin hanci a hannun kamfanin saboda a yi wa tufkar hanci.

Amma kwararre a fanin Diflomasiyar kasa da kasa kuma Malami a Jami'ar Abuja Dr. Farouk Bibi Farouk ya yi bayani cewa wannan zargi zai kara bata wa Najeriya suna a idon duniya, domin zai kara bayyana gazawar gwamnati wajen binciken Laifukan cin hanci da rashawa da ake ganin gwamnati tana da tabo a idanun Duniya.

Farouk ya ce maimakon gwamnati ta mika wa ma'aikatar watsa labarai lamarin domin ta mayar da martani, kamata ya yi ta yi binciken gaggawa kan zargin.

Da Muryar Amurka ta tuntubi wasu ‘yan Majalisa kan lamarin, sai suka yi gum, babu wanda ya yarda ya yi magana.

Gwamnati za ta ci gaba da bibiyar shari'ar aikata laifuka kan kamfanin na Binance a ranan 17 ga wannan wata.

Saurari cikakken rahoto daga Medina Dauda:

Gwamnatin Najeriya Ta Musanta Zargin Neman Cin Hancin Dala Miliyan 150 Daga Kamfanin Binance.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG