Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Umarci Ma'aikatanta Da Su Fara Aiki Daga Gida


Shugaba Buhari
Shugaba Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta umarci dukkanin ma'aikatanta da su fara aiki daga gida domin takaita yaduwar cutar Coronavirus.

Mai taimaka wa Shugaban kasar kan harkokin yada labarai Bashir Ahmed ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter.

A cewar sakon dukkanin ma'aikata, daga matakin albashi na 12 zuwa kasa za su fara aiki daga gida tun daga ranar 24 ga watan nan na Maris.

Sakon ya kara da cewa wannnan na daya daga cikin matakan da gwamnatin ta dauka domin karfafa yaki da wannan annobar ta coronavirus.

Hakan na zuwa ne a dai-dai lokacin da aka samu mutum na farko wanda ya rasa ransa sakamakon wannan cutar.

Mutum 40 ne dai suka kamu da Cutar a kasar ta Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG