An samu matsaloli da sunayen ciki har da na rashin amincewar wasu da karbar mukamin kamar yadda Polin Talin tayi saboda rashin lafiyar mijinta.
Malam Garba Shehu yace abu na jama'a dole ne a yi korafe-korafe. Yace an sa ido domin akwai bukatu na gwamnonin jihohi da manyan 'yan siyasa da masu mulki da wadanda suka san abun da aka yi dasu can baya da suke ganin sun isa su sa a yi.
Tunda aka ce mutane arba'in da biyu za'a fitar ba kowa ba ne zai samu yadda ransa yake so ba. Inji Malam Garba Shehu koda an kai sabbin sunaye Majalisar Dattawa za'a sake samun gaddama akansu. Saidai a duba kasar a kyautata domin a cigaba da ayyuka.
Yace a fahimtarsa za'a sake mayarwa Majalisar Dattawa sunayen da aka daidaita domin a tantancesu su tafi su wakilci Najeriya a kasashen waje.
Wani batun da majalisar zartaswa zata yi nazari a kai shi ne na mukaddashin shugaban hukumar EFCC tunda Majalisar Dattawa ta ki amincewa da sunan Ibrahim Magu sanadiyar rahoton tsaro da hukumar DSS ta bayar a kansa.
Ita Majalisar Dattawa tace dole ne ta tantance duk sunan da aka kawo mata saboda haka ba zata yi aiki cikin gaggawa ba, wato a bata suna yau a ce ta amince nan take ba zata yiwu ba.
Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.