Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Neja ta Rufe Wasu Makarantu dake Zaman Kansu


Yara cikin wani ajin karatu

Saboda rashin bin ka'ida gwamnatin jihar neja ta rufe wasu makarantu fiye da 120.

Daga bara zuwa yanzu sama da makarantu 120 masu zaman kansu gwamnatin jihar Neja ta rufe saboda kasawarsu na cika kai'idodin da aka gindiya masu.

Darakta a ma'aikatar ilimi ta jihar Malam Isa Jibril yace an dauki matakan ne saboda basu cika ka'idojin da aka basu ba kafin su bude makarantun.

Malam Zuberu S.D. na Kwalajin Sudan dake Kontagora yace kafin a yadda mutum ya bude makaranta sai masu sa ido sun ga wurin sun kuma amince.

Saidai kungiyar masu makarantu dake zaman kansu sun ce sun gamsu da tanadin da suka yiwa makarantunsu.

Alhaji Danladi Kowa shugaban makarantar Kowa dake Minna babban birnin jihar, kuma shugaban kungiyar masu makarantun dake zaman kansu yace sun amince da matakan da gwamnati ta dauka saboda da zara mutum ya samu cancanta gwamnati zata bada goyon baya.

Wasu makarantun basu cancanta ba. Wasu ma sun fara ne a cikin shaguna abun da bai kamata ba.

Malam Idris Adarawa na Kwalajin Sudan yace kara sawa malamai idanu zai yi tasiri a makarantu masu zaman kansu. A tabbatar an samu kayan aiki isassu da kuma hadin kan jama'a.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Shiga Kai Tsaye

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG