Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Samar da Makarantu a Sansanonin 'Yan Gudun Hijira a Jihar Adamawa


Jama'an da suka kauracewa gidajensu biyo bayan harin 'yan Boko Haram, sun samu mafaka a wata Makaranta, a Maiduguri. (File Photo)

Ana kokarin samarma 'yayan masu gudun hijira makarantu na wucin gadi a yanki Arewa maso gabas.

Hukumar taimakon agaji ta gaggawa a yankin Arewa maso gabas wato NEMA, sun fito da wani tsari na bude makarantu a sansanonin ‘yan gudun hijira a jihohin yankunan, wadan da rikicin boko haram yasa suka bar gidajen su. Acewar me kula da sansanonin a jihar Adamawa Alh. Sa’adu Bello, an kirkiro da wannan ne don taimakama wadanda ke a wadanan sansanonin don kada a barsu a baya, don su yi daidaito da sauran yara.

Kuma gwamnatin tarayya ta fito da wani shiri mai suna Hanyoyin tattala makarantu (Save Schools Initiatives) a turance, wanda wannan damace ta bama wadannan yaran dama don su tafi wasu garuruwa wadanda basu fama da wannan matsalolin don cigaba da karatunsu.

Don samun daurewa ga koyar da wannan yaran ‘yayan ‘yan gudun hijiran, Shugaban hukumar agajin gaggawa ta jihar Adamawa SEMA Alh. Haruna Hammanfure, ya bayyanar da cewar hukumar tasu ta yi kokarin samar da malamai da ‘yan sakai, kasancewar cikin wadan da suke aikin hadin gwida da su akwai malamai, kuma wasu da ga ciki na da sha’awar koyarwa. Yace zasu cigaba da kokarin ganin a koyar da wannan yaran da kuma kokarin bin tsari na ajujuwa da shekarun yaran koda kuwa a karkashin bishiyar mangoro ne.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00

XS
SM
MD
LG