Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nigeria Ta Kebe N1.7tr Domin Shirin Ci Gaban Kasa PEWASH


Shugaban Nigeria Muhammad Buhari
Shugaban Nigeria Muhammad Buhari

Sabon shirin ciyar da kasar gaba da zai lakume zunzurutun kudi har Nera tiriliyon daya da miliyan dubu dari bakwai na hadin gwuiwa ne tsakanin gwamnatin tarayyar Nigeria da jihohi.

Shirin na Gwamnatin Tarayya mai taken PEWASH dake mayar da hankali wajen samar da ruwa, tsabtar muhalli da na jiki, da ma'aikatar ruwa ta Najeriya ke jagoranta, na da zummar cimma "dawwamammun muradun Karni" masu dorewa da ake kira [SUSTAINABLE DEVELOPMENT GOALS], da turanci. Shirin da tuni gwamnatin tarayya ta kebe wa Naira Triliyan daya da Milyan dari bakwai don tabbatar da nasararsa.

Jihar Kano ce ta biyu a Tarayyar Nigeria wajen rungumar shirin gadan gadan, inda gwamnatin jihar ta sanya hannu bisa yarjejeniyar aiki tare da ma'aikatar ruwa ta kasa. Gwamnan jahar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya shaidawa Muryar Amurka Muhimmancin shirin a garesu inda ya ce ''Muhimmancinsa yana da yawa kwarai da gaske, tunda in an yi maganar ruwan sha ai an yi maganar rayuwa kenan, kuma in an yi maganar tsabtace muhalli da kuma kula da lafiya, wadannan ababe in ka hadasu to kaga abin da mutane suke bukata kenan, musamman in kasan irin abubuwan da suke faruwa a kauyukanmu to za ka san cewa wannan tsari da aka dauko,tsari ne da zai kyautata rayuwa a Nigeria musammanma mu a nan arewa""

A baya dai shirin cimma muradun karni da ake kira MDGs a takaice, bai sami cikakkiyar nasara ba a Nigeria, kuma gashi yanzu an dora da ci gaban shirin wato shirin ci gaba mai dorewa na SDGs, ko me ya kawo tarnaki a shirin farko na MDGs din? Ministan albarkatun ruwa na Nigeria Injiniya Sulymanu Hussaini Adamu, ya ce batu ne na kasafin kudi, abin kenan da ya sa gwamnatin tarayya da na jihohi suka fito da wani tsari na zayyana irin rawar da kowane bangare zai taka,

Misali inji Minista Sulayman Adamu,an daddale abin da gwamnatin Tarayya za ta yi da kuma wanda gwamnatin jiha za ta yi.Idan gwamnatin jiha taki sauke nauyin da ke kanta sai gwamnatin Tarayya ma ta noke. Yaci gaba da cewa an yi hakan ne da nufin ganin ba a sami matsalar da aka samu ba a baya. A naso ne don a kara zumma akan abin a taimakawa mutane dangane da batun harkar ruwan sha.

A saurari rahoton Hassan Maina Kaina domin karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:12 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG