Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar DSS Ta Bayyana Yadda Mal Lawal Daura Ya keta Ka'idojin Gwamnati


Sabon direkta Janar din hukumar leken asirin Najeriya DSS Mr Mathew Seyeifa ya gana da manema labarun Najeriya inda ya bayyana matakan da zai dauka na inganta aikin hukumar.

Bayan da mukkadashin shugaban Najeriya farfesa Yemi Osinbanjo ya kori mal Lawal Daura a matsayin sa na shugaban hukumar leken asiri ta kasa wato DSS. aka kuma nada Mr Mathew Seyeifa domin ya maye gurbin sa, sabon direkta general din ya gana da manema labaru a Najeriya in da ya tabbatar wa 'yan kasa zai bi ka’idoji na doka wurin kudanar da aikin sa.

Sabon darektan ya kuma ce za a tabbtarar duk wadanda ke tsare a hannun hukumar an bi doka wurin yi masu shari'a ko a sake su idan hukumar ta tarar basu da laifi.

Wannan jawabi dai yana zuwa ne a dai dai lokacin da 'yan Najeriya ke cigaba da tsokacin akan ‘yan’uwan su ko abokai da aka kama aka tsare ba tare da bin ka'idoji na doka ba duk da yake a wadansu lokuta kotu tana bada umarnin sakinsu.

Ana dai zargi Mal Lawal Daura da cigaba da rike mutanen da kotu ta bada umarnin sakinsu ba tare da bin kai’da ko hukunce hukunce na kotu ba.

A cikin hirarsu da Sashen hausa, wani lauya mai fafutukar kare hakin bil adama kuma daya daga cikin lawyoyin da suke da irin wannan koken akan Mal Lawal Daura wato Bar. Abdulhamid Muhammed, yayi karin haske dangane da muhimmanci sanarwa da Mr mathew Seyeifa Sabon mukadashin shugaban hukumar leken Asiri ta kasa wato DSS yayi.

Saurari cikakken rahoton Umar Faruk Musa

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG